Kungiyar kwadagon Najeriya ta fasa tafiya yajin aiki

Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun janye yajin aikin gama gari kan farashin wutar lantarki bayan tattaunawa da gwamnati.
Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar, Festus Keyamo, ya ce an dakatar da aikin da aka shirya farawa a yau bayan an cimma yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon da sanyin safiya.
Mista Keyamo ya ce gwamnati da kungiyoyin kwadago sun amince su tattauna a kan farashin wutar lantarki a cikin makonni biyu masu zuwa.
A da dai kungiyoyin kwadagon sun ce ba za a yi ayyuka a ma'aikatun gwamnati da bankuna da kuma filayen jiragen sama ba, haka kuma ana ganin yajin aikin zai shafi asibitoci da sufurin motoci.

Babbar manufar yajin aikin ita ce domin su karawa matsawa gwanati lamba a kan ta janye matakan da ta dauka a baya-bayannan da suka jibanci tattalin arziki.
Matakan kuwa sun hadar da cire tallafin da gwamnatin ke bayarwa a kan farashin man fetir abin da ya janyo farashin man ya karu da kimanin kashi 11 cikin 100.
Akwai kuma matakin ninka farashin wutar lantarki da aka yi wanda tuni ya fara janyo guna-guni daga 'yan kasar wadanda ke cewa kamfanonin rarraba wutar lantarkin sun fara tsuga musu kudin wutar da ya wuce tunaninsu.
Tuni dai gwamnatin Najeryar ta ce, ya zama wajibi ta dauki wadannan matakai domin tallafawa tattalin arzikin kasar da kuma tsimin kudaden shiga saboda tattalin arzikin ya gamu da illa sakamakon faduwar farashin danyen man fetir a kasuwar duniya.

_bbchausa

Comments

Popular posts from this blog

VIDEO : Hamisu Breaker Tarihin Rayuwarsa Da Dalilin Zama Mawaki da Kuma wakar Da Yafi So (kalli bidiyo)