Ina karanta littafin wani Bature kan zaben sabon Sarkin Zazzau - El-Rufa'i

Gwamnan Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya ce yayin da ya ke jiran sunaye daga masu zaɓen sarkin Zazzau, yana karanta wani tsohon littafi na wani Farfesa farar fata kan zaɓen sabon sarkin Zazzau.

A shafinsa na Twitter, El-Rufa'i ya wallafa hoton bangon littafin da Farfesa M G Smith ya rubuta mai taken "Gwamnati a Zazzau." wanda aka buga a 1960.

Gwamna El- Rufa'i ya ce littafin da ke bayani kan zaɓen sarakunan Zazzau daga 1800 zuwa 1950 zai masa jagora wajen yanke shawarar zaɓen sabon sarkin Zazzau, tattarawa bbchausa

Comments

Popular posts from this blog

VIDEO : Hamisu Breaker Tarihin Rayuwarsa Da Dalilin Zama Mawaki da Kuma wakar Da Yafi So (kalli bidiyo)