Hawau :Bayan ganawa da sarauniyyar Ingila Bill Gates ya yiwa 'yar Najeriya gagarumar kyauta

Wata yar Najeriya ta samu kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill and Melinda Gates ta shekarar 2020

- Hauwa Ojeifo, ta samu kyautar ne sakamakon gudumawar da take bayarwa wurin daidaiton jinsi bayan fuskantar cin zarafi ta da taba yi

- Matar ta samu jinjinar Queen's Young Leaders sakamakon lura da kokarinta wurin jawo masu matsalar kwakwalwa a jikinta da kuma basu kwarin guiwa

Wata 'yar Najeriya mai suna Hauwa Ojeifo ta samu gagarumar kyauta ta musamman daga gidauniyar Bill Gates da Melinda Gates ta shekarar 2020.

Kasancewar budurwar mai rajin kare hakkin jinsi da nakasassu ce, tana jagorantar wata kungiya mai taimako da bada shawarwari ga masu fama da rashin lafiyar kwakwalwa.

Hauwa Ojeifo tana bawa masu damuwa karfin gwuiwa ne ta hanyar basu labarin rayuwarta da irin kalubalen da ta fuskanta.



Jaridar Legit.ng ta tattara bayanai daga gidauniyar a ranar Talata, 22 ga watan Satumba dake nuna yadda Hauwa tayi fice a ayyukan ta na daidaiton jinsi da taimakon masu matsalar kwakwalwa.

Ta samu jinjinar ne tun bayan kula da akayi da yadda take taimakon masu cutar tabin hankali kuma tana hana mutane kyamatar su.

Ta zama yar Najeriya ta farko da ta samu wannan gagarumar kyauta ta jinjina


Shi kuwa biloniyan dan kasuwa Charles Chuck Feeney a karshe dai ya cika burinshi na rayuwa, inda ya dinga addu'ar ya talauce tun yana da rai, a karshe dai hamshakin mai kudin ya bayar da dukiyarshi sadaka baki daya.

Mutumin wanda ya samar da kamfanin Duty Free Shoppers, ya ce akwai dadi sosai idan ka bayar da dukiyar ka tun kana raye ba wai sai ka mutu ba.

Comments

Popular posts from this blog

VIDEO : Hamisu Breaker Tarihin Rayuwarsa Da Dalilin Zama Mawaki da Kuma wakar Da Yafi So (kalli bidiyo)