Ga Wata Alfarma Ga Matasa Domin Samun Rance Na Kudi Daga Shugaba Buhari



Idan matasa basu manta ba; ranar 23 ga watan shida (July)  na wannan shekarar, shugaban kasa Muhammadu Buhari Maigaskiya ya amince a fitar da kudi Naira biliyan 75 domin tallafawa matasan Nigeria maza da mata da rancen kudin domin su bunkasa kasuwancin su da sana'o'in su
Wannan kudi ana so a bayar da shi gaba daya a cikin shekaru uku, kowace shekara za'a fitar da Naira biliyan 25, za'a fara daga wannan shekarar ta 2020 Insha Allah
Ta yaya za'a samu wannan rancen?
Ga mai bukata ya shiga shiga wannan website din www.youthsandsport.gov.ng
Ko kuma
www.noya.ng
Aayi yi rijista da ma'aikatar matasa da wasanni
(Ministry of Youths and Sports).
Idan an shiga website din anyi rijista zasu tuntube ka nan gaba ta email dinka, ko ta lambar wayarka idan za'a fara bayar da rance.
Abubuwan da ake bukata:

1. Active email, email wanda yake aiki.
2. Lambar waya.
3. Address.
4. Wadanda zasu cika, maza ko Mata, daga shekara 18 zuwa 35.
5. CAC registration number.
Amma idan baka da CAC Number, baka taba rijista da hukumar ba, to ka tsallake shi kawai, registration din zai yiwu ko baka da lambar CAC din..

Allah Ya sa duk wanda ya cika ya dace.
Allah Ya taimaki wannan shugaba namu Dattijon kwarai Muhammadu Buhari mai kokari da son taimakawa al'umma musamman matasan da suka yi masa wahala suka zabe shi.
Masharurin marubucin nan Datti Assalafy yayi wannan rubutu.

Comments

Popular posts from this blog

VIDEO : Hamisu Breaker Tarihin Rayuwarsa Da Dalilin Zama Mawaki da Kuma wakar Da Yafi So (kalli bidiyo)