Posts

Image
 

#EndSars: 'Yan Najeriya sun yaba wa shahararren Jeremiah Omoto Fufeyin Sahihancin Annabta game da zanga-zangar "-Aproko Afrika

Image
#EndSars: Annabi Fufeyin ya yi kira ga ‘yan Nijeriya, Malaman Addini, mata su hada hannu wajen yin addu’o’i don yaki da yakin basasa  Biyo bayan zanga-zangar da ta barke a fadin kasar don neman kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda, musamman wani bangare na rundunar da ake kira Special Anti-Robbery Squad (SARS), fitaccen malamin addinin nan, Annabi Jeremiah Fufeyin ya yi kira ga ilahirin kungiyar kiristocin, musamman malamai su yi addu’a a kan yakin basasa.  Za a iya tuna cewa sanannen Annabin ya ga wannan yana zuwa a cikin 22 na Yuni, 2020 kuma ya yi kira ga coci su yi addu'a, daidaitar kalmomin annabcinsa ya sa mutane da yawa mamakin cikawa. Da yake magana a cikin wani bidiyo                    ya bayyana wa manema labarai, annabin ya ce dole ne ‘yan Najeriya su dage da addu’a, yana mai cewa yin shiru kan lamarin na nuna halakarwa.  “Kar kayi shiru. Abubuwa suna faruwa ta yadda ba za'a iya shawo kansu ba. Idan kuna tunanin abubuwan da ke faruwa a Edo, Lagos, Ribas, Delta, Ibada

Bidiyo: Allah Sarki!! Kalli Yadda Gwamna Zulum Ya Koma Maiduguri Bayan Kai Masa Hari A Baga

Image
Wannan shine yadda al'ummar jahar borno nazo tarbon farfesa babagana umara zulum wanda yayi kwana biyu a garin Baga. Wanda zaku ga irin yadda al'ummarsa ke matukar kaunarsa wanda abun zai yi matukar baka sha'awa. Ga bidiyon nan kasa. Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Kungiyar kwadagon Najeriya ta fasa tafiya yajin aiki

Image
Kungiyoyin kwadagon Najeriya sun janye yajin aikin gama gari kan farashin wutar lantarki bayan tattaunawa da gwamnati. Ministan kwadago da samar da aikin yi na kasar, Festus Keyamo, ya ce an dakatar da aikin da aka shirya farawa a yau bayan an cimma yarjejeniya da kungiyoyin kwadagon da sanyin safiya. Mista Keyamo ya ce gwamnati da kungiyoyin kwadago sun amince su tattauna a kan farashin wutar lantarki a cikin makonni biyu masu zuwa. A da dai kungiyoyin kwadagon sun ce ba za a yi ayyuka a ma'aikatun gwamnati da bankuna da kuma filayen jiragen sama ba, haka kuma ana ganin yajin aikin zai shafi asibitoci da sufurin motoci. Babbar manufar yajin aikin ita ce domin su karawa matsawa gwanati lamba a kan ta janye matakan da ta dauka a baya-bayannan da suka jibanci tattalin arziki. Matakan kuwa sun hadar da cire tallafin da gwamnatin ke bayarwa a kan farashin man fetir abin da ya janyo farashin man ya karu da kimanin kashi 11 cikin 100. Akwai kuma matakin ninka

An fara yajin aikin sai baba ta gani a Najeriya

Image
A ranar Litinin 28 ga watan Satumba,2020 ne, ƙungiyoyin ƙwadago a Najeriya ke fara yajin aikin sai baba ta gani a fadin ƙasar don nuna rashin amincewarsu da ninka farashin wutar lantarki, da ƙarin farashin man fetur da kuma abin da suka kira tsadar rayuwa. Kungiyoyin kwadagon sun bayyana cewa ƙarin farashin zai daɗa jefa talakawan Najeriya cikin wahala. Ana sa ran yajin aikin sai na abin da hali ya yi wanda hadaddiyar kungiyar kwadago ta Najeriya ke jagoranta a fadin kasar zai kassara ayyuka a bangaren gwamnati da ma bangaren masu zaman kansu. Kungiyoyin kwadagon sun ce ba za a yi ayyuka a ma'aikatun gwamnati da bankuna da kuma filayen jiragen sama ba, haka kuma ana ganin yajin aikin zai shafi asibitoci da sufurin motoci. Bbchausa ta kara da cewa,Kazalika kungiyoyin kwadago da na farar hula za su gudanar da zanga-zangar lumana a manyen biranen kasar ciki har da Abuja babban birnin tarayyar Najeriyar. Babbar manufar yajin aikin ita ce domin su karawa matsawa

Gaskiyar Hari da anka kaiwa Gwamna zulum A yau Da Video da Yawo cewa shine A kwance

Image
Alhamdulillahi a yau mun samu daga kafar yada labarai mai suna vob ma'ana voice of borno ta wallafa gaskia al'ammari a shafin na facebook. Ga bayyaninta nan (1)Ana ta ci gaba da yada'wa cewa an kai hari akaro na 2 biyu kan tawagar  Mai Girma Gwamnan a yayin  da'aowar sa a sakanin Baga da Monguno tofa kanzan kuregr na. (2)Kuma anyi ta yada Video dake nuna wai Mai Girma Gwamnan yana kwance rub da ciki yayin arta'bu sakanin BH da jamian tsaro to shima sha shatau ne. Hakaza Mai Girma Gwamnan a nan birnin Maiduguri a jirgi mai saukar ungulu ya isa garin Domin samin gamsuwa kafi tawagogin 2 su isa garin Baga Ma'ana Baya cikin tragar da aka kai Hari balen tana a dauki video. Voice of Borno.. Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Bidiyo : Gani Ya Kori Ji : Kalli Bidiyon Wannan Ƙaramin Yaro Yana Bayyanin Irin Yaki Da Ta'addancin Boko Haram Da ya halarta

Image
Innalillahi Wa Innaa Ilaihi Raji'unn Shekaran jiya juma'a Civilian JTF suka samu nasaran kama wannan yaro wanda ya samu horo a kan ayyukan ta'addancin kungiyar Boko Haram bayan ya shigo cikin garin Maiduguri daga jeji Yaron yayi bayanin irin yakukuwa da ya halarta da Boko Haram, da yadda suke hallaka mutane, da yadda suke samun bayanan sirri daga gurin maciya amanar tsaron Nigeria da suke buya a cikin gari da irin kudaden da ake biyansu, hiran da akayi da yaron ya kai kusan mintuna biyar, amma na yanke bidiyon saboda nauyinsa Yaron yace babu wani abun da zai faru a Nigeria ba'a sanar dasu a jeji ba, duk wani shiri da hukumomin tsaro suke yi a boye ana tura musu da bayanai da bidiyo daga cikin gari, yace akwai wani soja yana da zama a barikin sojoji dake Maimalari, sojan ne yake tura masu da dukkab bayanan sirri suna biyanshi da kaso 50 na kudin da suke samu Shafin Datti Assalafy ne ya wallafa,yanzu haka an mika yaron hannun Intelligence officers a Maiduguri,